Rosicky ya yi ritaya daga buga tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rosicky ya ci kofin FA a Arsenal da Bundesliga a Dortmund

Tsohon dan wasan Arsenal, Thomas Rosicky ya yi ritaya daga buga kwallon kafa a kungiyar Sparta Prague wacce ya fara yi wa tamaula tun yana matashin dan kwallo.

Daga nan ne Rosicky ya koma Borussia Dortmund da murza-leda a 2001, sannan ya koma Arsenal a shekarar 2006.

Rosicky mai shekara 37 ya koma Sparta a 2016, inda ya yi wasa 12 kacal sakamakon rauni da yake fama da shi.

Dan kwallon ya fara buga wa Jamhuriyar Czech tamaula yana da shekara 19, yanzu shi ne wanda yafi yawan buga wa kasar wasanni, bayan da ya yi 105.

Rosicky ya lashe kofin Bundesliga a Dortmund da kuma FA biyu a Arsenal.