AFCON 2019: CAF ta kara jan kunnen Kamaru

CAF Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kamaru ce ke rike da kofin nahiyar Afirka da ta ci a 2017 a Gabon

Shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, Caf, Ahmad ya kara jaddada jan kunnen Kamaru kan karbar bakuncin gasar cin Kofin Afirka ta 2019.

A lokacin da ya amsa tambayar da aka yi masa kan ko Kamaru za ta iya karbar bakuncin gasar da za a yi ta kasashe 24, ya ce idan kasar ba za ta iya ba, sai su nemi wacce za ta maye gurbinta.

Sai dai ya ce mahukuntan kasar tun daga shugaban kasa zuwa kasa suna tabbatar musu da cewar za su iya karbar bakuncin wasannin.

Tun kafin hukumar ta CAF ta sauya tsarin buga gasar daga kasashe 16 zuwa 24, ministan wasannin Kamaru, Isma'il Bidoung ya karyata batun cewar an bar kasar a baya wajen shirye-shirye.

A cikin watan Agusta aka sa ran wani kamfanin bincike mai zaman kansa ya kamata ya duba shirye-shiryen Kamaru, amma sai ya janye yin hakan ba tare da wasu dalilai ba.

Yanzu dai an tsayar da farkon shekara mai zuwa domin kai ziyarar aiki Kamaru kan shirye-shiryen da take yi na karbar bakuncin gasar cin kofin na Afirka da za a yi a 2019.