Wenger ya nemi daukar fansa kan Liverpool

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool tana mataki na hudu a kan teburin Premier, yayin da Arsenal ce ta biyar

Arsene Wenger ya bukaci 'yan wasan Arsenal da su dauki fansa a kan Liverpool kan doke su da ta yi a farkon fara gasar cin kofin Premier ta bana.

Liverpool, wacce Jurgen Klopp ke horaswa, ta ci Arsenal 4-0 a Anfield a gasar Premier da suka fafata a watan Agusta.

'Yan wasan Liverpool da suka ci kwallayen a karawar sun hada da Roberto Firmino da Sadio da Mohamed Salah da kuma Daniel Sturridge.

Bayan da aka buga wasa 18 a gasar Premier, Liverpool tana mataki na hudu da maki 34, ita kuwa Arsenal ita ce ta biyar da maki 33.

Arsenal za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na 19 a gasar Premier ta bana.