Senegal ce ta daya a kwallon kafar Afirka

Senegal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Senegal daya ce daga tawagar Afirka biyar da za su buga kofin duniya a Rasha a 2018

Tawagar kwallon kafa ta Senegal ta ci gaba da zama ta daya a fagen murza leda a Afirka a jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta fitar a ranar Alhamis.

A jadawalin da hukumar ta bayyana a shafinta na intanet ya nuna Senegal, wacce za ta wakilci Afirka a gasar kofin duniya, tana ta 23 a duniya.

Tunisia ce ta biyu a Afirka sai Masar ta uku, Jamhuriyar Congo da Morocco da Burkina Faso da Kamaru da Ghana da Nigeria da Algeria cikin jerin goman farko.

Har yanzu Jamus ce ta daya a duniya sai Brazil ta biyu Portugal ta uku sannan Argentina da Belgium ta biyar.