Manchester City za ta dauki Sanchez

Sanchez Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City tana mataki na daya a kan teburin Premier, ita kuwa Arsenal tana ta biyar.

Har yanzu Manchester City na son sayen Alexis Sanchez daga Arsenal, amma za ta jira har zuwa karshen kakar wasa ta bana kafin ta neme shi.

A karshen kakar shekarar nan kwantiragin Sanchez dan kasar Chile da Arsenal zai kare.

A cikin watan Agusta ne Arsenal ta amince da tayin da City ta yi wa Sanchez mai shekara 29 a ranar da za a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai, amma daga baya maganar ta bi ruwa.

Haka kuma City tana fargaba idan ta sayo Sanchez a watan Janairu, ba ta da tabbas kan gurbin da zai buga mata tamaula, ganin yadda 'yan wasanta ke kokari.

Tuni dai kocin City, Pep Guardiola ya tattauna da mahukuntan kungiyar Ettihad kan 'yan wasan da yake son saya nan da wata 18.

Manchester City tana mataki na daya a kan teburin Premier na bana, bayan da aka yi wasa 18, ta kuma bai wa Manchester United wacce take ta biyu tazarar maki 11.