Morata ba zai buga wa Chelsea wasa ba

Chelsea Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda Morata ya yi murnar kwallon da ya ci Bournemouth

Alvaro Morota ba zai buga wa Chelsea wasan Premier da za ta ziyarci Everton a ranar Asabar ba, sakamakon katin gargadi da aka ba shi a karawa da Bournemouth.

A ranar Laraba Chelsea ta ci Bournemouth 2-1 a gasar kofin Carabao, kuma a lokacin da Morata ya ci kwallo ya dauka ya saka a cikin rigarsa sannan ya sa yatsansa na hagu a baki ya kuma yi nuni da daya hannunsa na dama da alama ta batanci.

Sai dai kuma matar Morata, Alice Campello ta sanar da cewar tana dauke da ciki, ne shi ya sa mijin nata ya yi hakan domin ya sanar wa duniya.

Halayyar da Morata ya nuna ta sa aka ba shi katin gargadi kuma na biyar da ya karba a kakar bana, hakan na nufin ba zai buga wasa daya ba kenan.

Chelsea za ta ziyarci Everton a Goodison Park a gasar Premier wasan mako na 19 a ranar Asabar 23 ga watan Disamba.