Barca ta bai wa Real tazarar maki 14

El Clasico Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barcelona wacce ke ta daya a kan teburi ta bai wa Real Madrid wacce ke mataki na hudu tazarar maki 14

Real Madrid ta yi rashin nasara a hannun Barcelona da ci 3-0 a wasan mako na 17 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu da suka kara a ranar Asabar.

Barcelona ta ci kwallo ta hannun Luis Suarez da Lionel Messi da kuma ta uku da Aleix Vidal ya ci daf da za a tashi daga karawar.

Lionel Messi shi ne yafi cin kwallo a tarihin karawar El Clasico, bayan da ya ci kwallo na 25, guda 15 a Bernabeu kuma 17 a gasar La Liga ta bana.

Real ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Dani Carvajal jan kati sakamakon taba kwallo da hannu a cikin da'ira ta 18 din Madrid

Da wannan sakamakon Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga da maki 45, ita kuwa Real Madrid mai rike da kofin tana ta hudu da maki 31.

Barcelona za ta karbi bakuncin Levante a wasan mako na 18 a ranar 7 ga watan Janairun 2018, a kuma ranar ce Real Madrid mai kwantan wasa daya za ta ziyarci Celta Vigo.