Hamsik ya buge tarihin Maradona

Serie A Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Marek Hamsik ya koma Napoli daga Brescia shekara 10 da ta wuce

Marek Hamsik ya buge tarihin da Diego Maradona tsohon dan wasan Argentina ya kafa na wanda yafi cin kwallaye a Napoli.

Napoli ta yi nasarar doke Sampdoria 3-2 a ranar Asabar a wasan mako na 18 a gasar cin kofin Serie A karawar mako na 18, kuma hakan ya sa ta ci gaba da zama ta daya a kan teburi.

Kyaftin din Napoli, Marek Hamsik shi ne ya ci kwallo na uku tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, kuma na 116 da ya ci wa kungiyar a wasa 465 da ya buga mata.

Tun a makon jiya ya yi kan-kan-kan da Maradona a yawan cin kwallaye a fafatawar da Napoli ta doke Torino 3-1, bayan ya buga wasa 13 bai ci kwallo ba a kungiyar.

Napoli ita ce ta daya a kan teburin Serie da maki 45, bayan wasa 18 da ta yi.