Messi ya ci kwallo 22 a kakar bana

Lionel Messi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga kuma Argentina za ta buga kofin duniya a 2018

Dan wasan tawagar kwallon kafa ta Argentina da Barcelona, Lionel Messi ya ci kwallo 22 a kakar 2017/18.

Messi ya fara zura kwallo ne a bana a karawar da Real Madrid ta doke Barcelona 3-1 a gasar Spanish Super Cup da suka kara a Nou Camp a ranar 13 ga watan Agustan 2017.

Daga nan ne dan wasan na Argentina ya ci biyu a fafatawar da Barcelona ta ci Alaves a ranar 26 ga watan Agustaa gasar La Liga.

Jumulla kwallo 22 Messi ya ci a kakar bana, 15 a gasar La Liga ya ci wa Barceloa, da hudu da ya zura a raga a gasar cin kofin Zakarun Turai da ukun da ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Argentina.

Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai, sannan Argentina za ta je gasar kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Labarai masu alaka