An ci kwallo 504 a gasar Premier Ingila

Premier week 19 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester City ce ke mataki na daya a kan teburin Premier bana

Bayan da aka kammala wasannin mako na 19 a ranar Asabar a gasar cin kofin Premier ta bana, an ci kwallo 504.

Gasar wacce aka fara a ranar 11 ga watan Agustan 2017, wacce kungiyoyi 20 ke fafatawa sun buga wasanni 190 kawo yanzu.

'Yan wasa biyu ne ke kan gaba a yawan cin kwallo a raga, inda Harry Kane na Tottenham da Mohamed Salah na Liverpool kowannensu ya ci kwallo 15.

Wasan da aka fi cin kwallaye a gida shi ne wanda Manchester City 5-0 Liverpool, Manchester City 5-0 Crystal Palace, Manchester City 7-2 Stoke City da na Arsenal 5-0 Huddersfield Town.

Manchester City wacce ke mataki na daya a kan teburi ta ci wasa 17 a jere, ta kuma yi 19 ba a doke ta ba.

Ita kuwa West Bromwich Albion wacce take ta 19 a kasan teburi ta yi wasa 17 ba tare da ta yi nasara ba a kakar ta bana.

Za a shiga wasannin mako na 20 a ranar Talata 26 ga watan Disamba:

  • Chelsea da Brighton & Hove Albion
  • Manchester United da Burnley
  • West Bromwich Albion da Everton
  • Watfordda Leicester City
  • Huddersfield Town da Stoke City
  • Bournemouth da West Ham United
  • Liverpool da Swansea City
  • Tottenham da Southampton

Labarai masu alaka