Ronaldo ya taka rawar gani a shekarar 2017

2017 Review Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shekara ta 2017 sai san barka ga wasu 'yan wasa da jami'ai da mahukunta, bayan da suka yi bajinta a fage da dama.

Haka kuma shekara ce da ta ci karo da kalubale a fanni da dama, ciki har da batun shan abubuwa masu kara kuzarin wasanni.

Wasu kuwa jami'ai da 'yan wasa ba su kai ga karshen shekarar ta 2017 da muke ban kwana da ita ba.

Mohammed Abdu Mam'man Skeeper ya yi bitar wasu daga cikin mahimman abubuwa da suka faru a shekara ta 2017

10 JANAIRU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta kara yawan kasashen da za su buga gasar cin kofin duniya. A bisa sabon tsarin, rukuni 16 mai tawagogi uku ko wanne za a samar a matakin farko kafin a kai matakin kifa-daya-kwala inda tawagogin da suka kai labari 32 za su fafata idan aka fara amfani da sauyin a gasar shekara ta 2026.

Hukumar kwallon kafar ta duniya ta yi ittifaki wajen kada kuri'ar amincewa da kawo sauyin ne yayin wata ganawar da a ka yi a birnin Zurich ranar Talata.

12 JANAIRU

Tsohon dan kwallon Ingila da Aston Villa wanda ya horar da Watford, Graham Taylor ya mutu sakamakon ciwon zuciya yana da shekara 72.

25 JANAIRU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya kwace lambar zinariya ta Nesta Carter dan kasar Jamaica, sakamakon samunsa da laifin shan abubuwa masu kara kuzari.

Nesta ya wakilci Jamaica a tseren mita 100 ta 'yan wasa hudu a gasar Olympic da aka yi a shekarar 2008, kuma kasar ce ta lashe tseren.

Sakamakon hakan ne yasa aka kwace lambar zinare guda hudun da 'yan wasan Jamaica suka ci a tseren mita 100 da aka yi a Beijing, cikinsu har da ta Usain Bolt.

Hakan kuma na nufin Bolt din ba shi ne dan wasa na farko da ya lashe lambobin zinare uku a jere a wasannin kakar Olympic uku ba.

28 JANAIRU

Serena Williams ta doke 'yar uwarta Venus da ci 6-4 da 6-4 a wasan karshe a gasar kwallon tennis ta Australian Open, inda hakan ya sa ta lashe babbar gasa ta 23.

29 JANAIRU

Carl Frampton ya rasa kambunsa na damben boksin na WBA ajin featherweight a hannun wanda ya karbi kambun Leo Santa Cruz, a dambatawar da suka yi karo na biyu a Las Vegas.

29 JANAIRU

Roger Federer ya doke Rafael Nadal ya kuma lashe gasar kwallon tennis ta Australian Open kuma babbar gasa ta 18 da ya lashe.

5 FABRAIRU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kasar Kamaru ta lashe gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka a karo na biyar bayan ta doke Masar da ci 2-1.

Vincent Aboubakar, wanda aka sako daga baya ne ya zura kwallon da ta ba su nasara minti biyu kafin a tashi daga wasan.

Tun da farko sai da dan wasan Kamaru Nicolas Nkoulou ya farke kwallon da Masar ta ci su, abin da ya bai wa 'yan wasan kwarin gwiwa.

23 FABRAIRU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Leicester City ta kori Claudio Ranieri kasa da shekara daya da kocin ya jagorancin kungiyar Lashe kofin Premier a karon farko a tarihi.

26 FABRAIRU

Zlatan Ibrahimovic ya taimakawa Manchester United ta lashe League Cup a Wembley, bayan da United ta doke Southampton 3-2.

08 MARIS

Barcelona ta kafa tarihin kungiyar tamaula ta farko da ta farke kwallo 4-0 a gasar cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League, bayan da ta ci Paris St Germain 6-1 a Camp Nou, inda Barcelona ta kai wasan zagaye na biyu da kwallaye 6-5.

28 MARIS

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta dakatar da Lionel Messi daga buga wa tawagar kwallon kafa ta Argentina wasa hudu.

Fifa ta hukunta dan wasan da ke taka-leda a Barcelona ne sakamakon samunsa da laifin yin kalaman cin mutunci ga mataimakin alkalin wasa a karawar da Argentina ta ci Chile 1-0.

Messi, wanda shi ne ya ci kwallo a fafatawar ta neman shiga gasar cin kofin duniya, ya yi fushi a lokacin da aka hura ya yi laifi, inda ya dinga yi wa mataimakin alkalin wasa surutai.

Haka kuma hukumar ta Fifa ta ci tarar Messi mai shekara 29 kudi fan 8,100.

29 MARIS

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Brazil, ta zama ta farko da ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Nasarar da Brazil ta doke Paraguay 3-0, da cin Argentina da Uruguay da aka yi ne, ya bai wa kasar damar ci gaba da zama ta daya a kan teburin Kudancin Amurka.

30 MARIS

Wanda ya kera butum-butumin Cristiano Ronaldo ya kalubalanci masu sukar aikin da ya yi, inda y ace Ronaldo ya amince da aikin da ya gabatar masa, yayin da ake cewar butum-butumin ya yi kama ne da Niall Quinn ba Ronaldo ba.

07 AFRILU

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kocin Celtic, Brendan Rodgers ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar bayan da ya ci wasa gasar kasar guda 10 a jere.

09 AFRILU

Shekara biyar bayan da Sergio Garcia ya ce bai da kwarewar da ta dace ya ci babbar gasar kwallon golf, sai gashi ya yi Justin Rose a gasar kwarru ya kuma lashe ta.

11 AFRILU

Aka kai wa motar Borussia Dortmund harin bam guda uku da ya raunata dan kwallonta mai tsaron baya, Marc Bartra, wanda hakan ya sa aka dage karawar da kungiyar ta yi niyyar yi da Monaco a gasar cin Kofin Zakarun Turai ta Champions League.

29 AFRILU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Anthony Joshua ya dambace Wladimir Klitschko, ita kuwa Katie Taylor ta ci wasan dambe na biyar a jere tun sanda ta zama kwararriyar 'yar wasa, inda ta doke Nina Meinke a fafatawar da suka yi Wembley.

'Yan kallo kimanin dubu 90 ne suka shaida karawar tsallen-baɗake, inda Joshua ɗan boksin ɗin Burtaniya, ya buge tsohon gwarzon duniyan a zagaye na biyar, kafin a kai shi ƙasa a zagaye na shida - karon farko a fafatawa 19 da ya yi.

01 MAYU

Mark Selby ya kare kambunsa na zakaran wasan Snooker na duniya, bayan da ya yi nasara a kan John Higgins da ci 18.

12 MAYU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chelsea ta lashe gasar Premier League a kakar farko da Antonio Conte ya fara jan ragamar kungiyar bayan da ta ci West Brom 1-0 duk da saura wasa biyu a kamala gasar

21 MAYU

Celtic ta kammala gasar cin kofin Scottish Premiership ba tare da an doke ta ba, inda ta ci Hearts 2-0 a wasan karshe.

22 MAYU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Juventus ta lashe kofin Serie A na Italia kuma na shida da ta dauka a jere, bayan da ta ci Crotone 3-0.

22 MAYU

Tsohon zakaran tseren motoci ta MotoGP na duniya Nicky Hayden ya mutu yana da shekara 35, kwana biyar da wata mota ta buge shi a lokacin da yake tuka keke a Italiya.

24 MAYU

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Manchester United ta doke Ajax 2-0 a Stockholm ta kuma lashe kofin Zakarun Turai na Europa.

27 MAYU

Arsenal ta hana Chelsea lashe kofi biyu bayan Premier da ta dauka, inda Gunners ta doke Chelsea 2-1 ta kuma lashe kofin FA Cup, kuma na 13 jumulla.

28 MAYU

Dan wasan Roma, Francesco Totti ya yi ritaya yana da shekara 40, bayan shekara 24 da ya yi a kungiyar, wacce ya buga wa tamaula sau 786 ya kuma ci kwallo 307.

3 YUNI

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe gasar zakarun Turai bayan ta doke Juventus da 4-1 a wasan karshen da suka buga a birnin Cardiff da ke Birtaniya. kuma kofi na 12 da ta lashe jumulla.

14 YUNI

Tsohon Zakaran damben boksin na duniya, Floyd Mayweather ya amince ya fafata da Conor McGregor, inda aka tsara wasan domin su kara a Las Vegas a ranar 26 ga watan Agusta.

16 YUNI

Brooks Koepka ya lashe gasar kwallon golt ta US Open, inda tsohon zakara Rory McIlroy ya kasa kai bantensa.

22 YUNI

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan kwallon Roma, Mohamed Salah ya je Liverpool domin a duba lafiyarsa, bayan da ya amince zai koma Anfield da murza-leda kan Euro miliyan 39.

26 YUNI

Tsohon dan wasan tawagar Holland, Frank De Boer ya zama kocin Crystal Palace kan yarjejeniyar shekara uku, sai dai wasa hudu kacal ya jagoranci kungiyar a gasar Premier.

10 YULI

Romelu Lukaku ya amince ya koma Manchester United daga Everton kan kudin da ake cewa zai iya kai wa fam miliyan 100. Shi kuwa Wayne Rooney ya koma tsohuwar kungiyarsa ta Everton duk a cikin kunshin yarjejeniyar sayen Lukaku.

15 YULI

Garbine Muguruza ta lashe babbar gasar kwallon tennis a karo na biyu, bayan da ta doke Venus Williams da ci 7-5 6-0 a wasan a gasar Wimbledon Open.

17 YULI

Manchester United ta doke Real Madrid a bugun fanareti bayan sun tashi a wasan gabannin kakarsu da ci 1-1 a Santa Clara.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Anthony Martial ne ya bai wa Jesse Lingard damar fara ci wa United kwallo daga gefen hagu.

Casemiro ya daukar wa Real Madrid fansa a bugun fenareti bayan sabon mai tsaron bayan United, Victor Lindelof, ya kayar da Theo Hernandez.

A bugun fanaretin da aka yi na raba gardama bayan an tashi wasan kunnen doki, an barar da fanareti 7 daga cikin 10 inda United ta doke Real Madrid da ci 2-1.

16 YULI

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Dan wasan tennis Roger Federer ya lashe kofin Wimbledon na bana bayan ya doke Marin Cilic.

Ya doke Cilic ne da ci 6-3 6-1 6-4, wanda rabon da ya lashe kofin tun a shekarar 2012.

Federer mai shekara 35 ya kafa tarihi na zama dan wasan tennis na farko a duniya da ya lashe kofin sau takwas.

Har ila yau, Federer wanda dan kasar Switzerland ne kuma shi ne dan wasa ma fi shekaru da ya lashe gasar Wimbledon tun bayan da aka sauya mata suna zuwa Open.

23 YULI

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Chris Froome ya ci gasar tseren keke ta Tour de France karo na hudu.

23 YULI

Jordan Spieth ya lashe gasar kwallon tennis da aka yi a Royal Birkdale, yana da shekara 23.

29 YULI

Aka soke damben Carl Frampton wanda ya so ya buga a karon farko bayan da ya rasa kambun WBA , bayan da abokin karawarsa Andres Gutierrez ya fadi a bandaki a Belfast inda ya ji rauni.

03 AGUSTA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Paris St-Germain ta kammala daukar Neymar daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a matsayin dan kwallo mafi tsada a tarihi a duniya.

Cinikin dan wasan na tawagar Brazil mai shekara 25, ya haura wanda Manchester United ta sayi Paul Pogba daga Juventus a Agustan 2016 kan fam miliyan 89.

Neymar zai karbi albashin fam miliyan 40.7 a shekara, za a biya shi fam 782,000 a duk mako kafin a cire haraji, kan yarjejeniyar shekara biyar.

03 AGUSTA

Tsohon zakaran damben boksin na duniya, Wladimir Klitschko ya sanar da yin ritaya, sannan ya karyata cewar ya bukaci ya sake dambatawa da Anthony Joshua.

6 AGUSTA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Justin Gatlin ya burge duniya inda ya yi wa zakaran tseren duniya Usain Bolt fintinkau a gasar 100m, kuma ya lashe lambar zinare.

An bar Bolt da tagulla a ranar da ya yi tserensa na karshe kafin yayi ritaya, inda Ba'amurke Christian Coleman mai shekara 21 yayi na biyu.

11 AGUSTA

Dan wasan Liverpool, Philippe Coutinho ya nemi izinin barin Anfield, bayan da Barcelona ta ce tana son sayen dan Kwallon na Brazil.

27 AGUSTA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Floyd Mayweather ya lashe dambensa na 50, bayan da ya yi nasara a kan Conor McGregor a turmi na 10 a dambatawar da suka yi a Las Vegas.

31 AGUSTA

Kylian Mbappe ya koma wasa Paris St Germain daga Monaco, tare da yarjejeniyar cewar PSG za ta iya sayen dan kwallon mai shekara 18 kan kudi Euro miliyan 180.

07 SATUMBA

Kungiyoyin Premier League suka amince a rufe kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon tamaula kwana daya kafin a fara kakar wasan 2018-19.

09 SATUMBA

Sloane Stephens ta lashe babbar gasar kwallon tennis a karon farko, inda ci gasar US Open, bayan da ta doke Madison Keys da ci 6-3 6-0.

9 SATUMBA

Hakkin mallakar hoto LMCNPFL

Kungiyar Plateau United ta ci kofin Firimiyar Nigeria na bana, bayan da ta doke Enugu Rangers 2-0 a wasan mako na 38 a ranar Asabar.

Emeka Umeh ne ya fara ci wa Plateau kwallo tun kafin aje hutun rabin lokaci, kuma bayan da aka dawo ne Benjamin Turba ya kara na biyu.

Hakan ya sa Plateau United ta hada maki 66 a wasa 38 da ta yi a gasar bana da rarar kwallaye 24.

13 SATUMBA

Kwamitin wasannin Olympic ya bai wa birnin Paris da na Los Angeles izinin karbar bakuncin gasar da za a yi a 2024 da kuma wacce za a kara a 2028.

08 OKTOBA

Hakkin mallakar hoto NFF

'Yan wasan Super Eagles na Najeriya suka samu tikitin zuwa wasan cin kofin duniya wanda za a yi a kasar Rasha 2018.

Nigeria ta yi nasarar cin Zambia 1-0 a fafatawar da suka yi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke jihar Akwa Ibom a kudancin Najeriya.

23 OKTOBA

Kungiyar Everton ta kori Ronald Koeman, bayan da kungiyar ta kasa taka rawar gani a wasannin shekarar nan.

23 OKTOBA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar dan kwallon kafa da babu kamarsa da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa ta karrama shi a 2017.

28 OKTOBA

Tawagar kwallon kafa ta Ingila ta yi nasarar lashe kofin matasa 'yan kasa da shekara 17, bayan da ta casa Spaniya da ci 5-2.

Tun farko Spaniya ta ci kwallo biyu ta hannun dan wasan Barcelona Sergio Gomez, sai dak kafin hutu Ingila ta zare daya ta hannun Rhian Brewster kuma na takwas da ya ci a gasar.

Daga nan ne Ingila ta samu kwarin gwiwa ta farke ta hannun Morgan Gibbs Wwhite wasa ya koma 2-2.

Ingila ta kara cin kwallo biyu ta hannun Phil Fodaen, sannan Marc Guehi ya ci na biyar.

29 OKTOBA

Hakkin mallakar hoto BBC Sport

Lewis Hamilton ya lashe gasar tseren motoci ta Formula 1 ta Mexican Grand Prix duk da kammala wasan a mataki na tara, bayan da ya yi karo da motar Sebastian Vettel.

Hamilton shi ne dan wasan da babu kamarsa a Burtaniya a wasan tseren motoci, ya kuma yi kan-kan-kan da Sebastian Vettel da Alain Prost wajen lashe gasar sau hudu.

Juan Manuel Fangio yana da tarihin lashe gasar sau biyar, yayin da Michael Schumacher ya dauka sau bakwai.

02 NUWAMBA

Dan wasan Marseille, Patrice Evra ya yi wa wani magoyin bayan kungiyar kafa a lokacin da 'yan wasa ke motsa jiki kafin karawa da Vitoria Guimaraes a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Europa.

04 NUWAMBA

Celtic ta karya tarihin da ta kafa shekara 100 da ta wuce, bayan da ta lashe wasa 63 ba tare da an doke ta ba, bayan da ta ci St Johnstone 4-0.

14 NUWAMBA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Mai tsaron ragar tawagar kwallon kafa ta Italiya, Gianluigi Buffon, yana zubar da hawaye ya nemi gafarar magoya bayan kasar, bayan da suka kasa samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya da za a yi a Rasha a 2018.

Kyaftin din ya yi ritaya daga buga wa Italiya tamaula, bayan da kasar ta kasa yin nasara a kan Sweden a wasannin da suka buga gida da waje don neman tikitin shiga gasar ta duniya.

Italiya ta tashi wasa babu ci da Sweden a gida, bayan da a wasan farko ta sha kashi da 1-0, hakan ne ya sa a karo na farko tun 1958 ba za a ga kasar a gasar ba.

01 DISAMBA

Aka raba jadawalin gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018.

7 DISAMBA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Ronaldo ya lashe Ballon d'or

11 DISAMBA

Dan wasan kasar Masar da kuma Liverpool, Mohamed Salah, ya ci kyautar gwarzon dan kwallon Afirka ta BBC ta shekarar 2017.

Bayan ya samu kuri'u masu tarin yawa, Muhamed Salah ya doke dan wasan Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da dan kasar Guinea Naby Keita da dan Senegal Sadio Mane da kuma dan Najeriya, Victor Moses.

17 DISAMBA

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin hukumar FIFA na kungiyoyin kwallon kafa na duniya inda ta doke kungiyar Gremio da ke kasar Brazil.

An dai buga wasan ne a birnin Abu Dhabi da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Asabar.

17 DISAMBA

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tsohon dan wasan kungiyoyin AC Milan da Real Madrid, Kaka, ya yi ritaya daga taka leda.

Yana daya daga cikin 'yan wasa takwas da suka lashe Kofin Zakarun Turai da Kofin Duniya da kuma kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'Or.

Dan wasan ya yi fice ne a iya yanka da zura kwallo a raga kuma ya zura kwallaye 29 a raga a wasannni 92 da ya buga wa kasarsa Brazil.

Labarai masu alaka