Yaya Toure ya yi amai ya lashe

Ivory Coast Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Toure ne kyaftin din tawagar Ivory Coast a lokacin da ta lashe kofin nahiyar Afirka a 2015

Dan wasan Manchester City, Yaya, Toure zai koma buga wa tawagar kwallon kafa ta Ivory Coast tamaula.

Dan kwallon mai shekara 34, ya yi ritaya daga buga wa kasar kwallon kafa a Satumbar 2016, bayan da ya yi mata wasa 100, sannan ya lashe kofin nahiyar Afirka a 2015 a tawagar.

Toure ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na Twitteer cewar ''Ina kyaunar kasata kuma a shirye nake na buga mata tamaula''.

''Ina son na taimakawa matasa da irin kwarewar da nake da ita, ta yadda Ivory Coast za ta yi alfahari da hakan''.

Toure, wanda ya koma Manchester City daga Barcelona a 2010, ya buga wa kungiyar da ke murza-leda a Ettihad wasa uku a gasar Premier a bana.

Ivory Coast ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a 2018 ba, amma tana shirin fara buga wasannin kai wa gasar kofin nahiyar Afirka a watan Maris.

Labarai masu alaka