Virgil van Dijk: Liverpool ta sayi dan wasan Southampton a kan £75m

Liverpool ta sayi Virgil Van Dijk daga Southampton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool ta sayi Virgil Van Dijk daga Southampton

Dan wasan Southamton Virgil van Dijk zai koma Liverpool ranar 1 ga Janairu da zarar an bude kasuwar cinikin 'yan wasa a kan fam miliyan 75.

Tun bara ake sa ran dan wasan dan asalin Holland zai koma Liverpool bayan da shi da kansa ya nemi a sayar da shi.

Amma hakan bai yiwu ba saboda an tuhumi Liverpool da zawarcin dan wasan ba tare da sanin kungiyarsa ba.

Kudin da za a biya Southampton ya fi na kowane dan wasan baya da aka taba saya a duniya.

Benjamin Mendy da Manchester City ta biya Monaco fam miliyan 52 a watan Yuli shi ne dan wasan baya mafi tsada kafin cinikin Dijk.

Van Dijk ya ce yana alfaharin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallo a duniya

A wata sanarwa da ya fitar, Van Dijk ya bayyana farin cikin komawarsa Liverpool.

"Ina matukar farin cikin komawa Liverpool a matsayin dan wasa. Yau rana ce ta alfahari a gare ni da iyalina a yayin da na ke shirin komawa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya."

"Na zaku da in saka jar rigar Liverpool da ta shahara a karon farko a gaban 'yan kallo, kuma na yi alkawarin sadaukar da kaina wajen taimaka wa wannan kungiyar cimma burinta a shekaru masu zuwa."