Man City ta kara fintinkau da maki 15 bayan doke Newcastle 1-0

'Yan wasan Manchester City na murna bayan da Raheem Sterling ya ci musu kwallo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rabon da Manchester City ta kasa cin wasanta a Premier tun lokacin da ta yi kunnen doki 1-1 da Everton a watan Agusta

Manchester City ta kara fintinkau da maki 15 a saman teburin Premier bayan da Raheem Sterling ya ci mata kwallo daya tilo da suka doke Newcastle.

Dan wasan gaban na gefe na Ingila ya zura kwallon ne a raga a minti na 31 bayan da Kevin de Bruyne ya zura masa ita, hakan ya kawo yawan bal din da ya ci wa City a kakar nan zuwa 17.

Tun kafin sannan sai da Sergio Aguero ya kusa ci bal din tana dukan karfen raga har sau biyu.

City ta ci gaba da kafa tarihin yawan nasara a gasar ta Premier ba tare da an doke ta ba, har zuwa wasanni 18 a jere, tare da jan ragaramar teburin gasar.

Rashin nasarar ga masu masaukin bakin shi ne na biyar a jere a gida, kuma hakan ya sa maki daya ne tsakaninsu da rukunin faduwa daga Premier.

Crystal Palace da Arsenal;

A ranar Alhamis din nan ne Arsenal za ta bakunci Crystal Palace inda za su yi wasansu na mako na 20 na gasar ta Premier da karfe 9:00 agogon Najeriya.