Swansea ta nada Carlos Carvalhal sabon kocinta

Swansea City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Carlos Carvalhal sabon kocin Swansea City

Swansea City da ke kasan teburin Premier ta nada tsohon mai horar da 'yan wasan Sheffield Carlos Carvalhal a matsayin sabon kocinta.

Carvalhal dan kasar Portugal zai ci gaba da horar da Swansea ne har zuwa karshen kaka amma da nufin tsawaita kwantaraginsa idan kakar ta yi kyau.

Swansea ta dauki Carvalhal ne bayan Sheffield da ke Lig mataki na biyu a Ingila ta sallame shi a jajibirin Kirsimeti yayin da kungiyar ke matsayi na 15 a tebur.

Yanzu shi ne mai horar da 'yan wasa na biyar da Swansea ta dauka a shekaru biyu bayan kungiyar ta kori Paul Clement.

A ranar Talata Liverpool ta lallasa Swansea 5-0 bayan kungiyar ta buga wasanni hudu tana shan kashi a premier.

Swansea City ce ta karshe a teburin premier, kuma babban kalubalen da ke gaban Carvalhal a yanzu shi ne farfado da kungiyar a teburin gasar.

Labarai masu alaka