Ba na tsoron tafiyar Sanchez duk da cin kwallon da yake - Wenger

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Arsene Wenger ya yaba wa Alexis Sanchez kan kwallo biyun da ya ci suka doke Newcastle 3-2

Arsene Wenger ya ce ba shi da wata damuwa a kan rasa Alexis Sanchez a watan Janairu, duk da kwallo biyu da dan wasan na gaba ya ci wa kungiyar da ta doke Crystal Palace 3-2.

Kwantiragin dan wasan na Chile zai kare ne da Arsenal a karshen kakar da ake ciki, kuma ana danganta dan wasan mai shekara 29 da tafiya jagorar Premier Manchester City, wadda ta kasa sayensa a karshen kakar da ta gabata.

Wenger wanda ya kamo tarihin da Sir Alex Ferguson ya kafa a Premier na jagorantar wasa 810 a gasar, ya ce shi kam ba shi da wata damuwa, illa dai abu ne da ya shafi kwantiragin dan wasan.

A wasan nasu da Newcastle bayan Andros Townsend ya farke kwallon da Shkodran Mustafi ya ci wa Arsenal a kashin farko na wasan ne, Sanchez ya zura kwallo biyu a cikin minti hudu a ragar masu masaukin bakin.

Mustafi ya fara daga ragar 'yan Newcastle a minti na 25 da wasa, amma Townsend ya farke a minti na 49, bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ke nan.

Daga nan ne kuma sai Sánchez din ya ci wa Arsenal ta biyu a minti na 62, sannan ya kara daga ragar bayan minti hudu.

Ana shirin tashi ne daga wasan sai kuma Tomkins ya ci wa Newcastle ta biyu a minti na 89.

Nasarar ta sa Gunners din sun ci gaba da zama a matsayi na shida da yawan maki 37 daidai da ta biyar Tottenham, kuma maki daya tsakaninta da ta hudu Liverpool.

Ita kuwa Newcastle tana matsayi na 16 a teburin na Premier bayan wasa 20.