Lukaku na bukatar hutu amma ba zai samu ba- Mourinho

Lukaku dan wasan Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lukaku tun zuwansa Manchester United ya buga wasannin Premier ba tare hutu ba

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ba zai iya ba Romelu Lukaku hutu ba duk da ya fahimci cewa dan wasan ya nuna "ya gaji".

Lukaku tun zuwansa ya buga wasannin Premier ba tare hutu ba, saboda jinyar raunin da Zlatan Ibrahimovic ya yi.

Dan wasan wanda ya koma United a bana kan kudi fam miliyan 75 daga Everton ya ci ma ta kwallo 11 a wasa 10 da ya yi, amma yanzu kwallaye hudu ya ci a wasanni 19.

"Yaron ya gaji amma yana da kyau har yanzu, ba zan iya ajiye shi ba" a cewar Mourinho.

A makwannin da suka gabata Lukaku ya tafka kurakurai da suka haddasa kwallayen da Manchester City da Burnley suka doke Manchester United.

Dan wasan ya dade yana fuskantar kalubale amma ba tare da Mourinho ya soke shi ba.

Tazarar maki 15 Manchester City ta ba Manchester United a teburin Premier, kuma a ranar Asabar 30 ga watan Disemba United za ta karbi bakuncin Southampton a Old Trafford.

Labarai masu alaka