Chelsea ta samu kudin da ba ta taba samu ba a shekara kusan naira biliyan 2

'Yan Chelsea na murnar cin kofin Premier Hakkin mallakar hoto OTHERS
Image caption Chelsea ta dauki kofin Premier a kakar da ta wuce, abin da ya ba ta damar dawowa gasar zakarun Turai

Mai rike da kofin Premier Chelsea, ta sanar da yin cinikin da ba ta taba yi ba na fam miliyan 361.3, kusan naira biliyan biyu a shekara nan ta 2017.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa ta ci ribar fam miliyan 15.3, wadda ta danganta da cinikin sayar da 'yan wasa na fam miliyan 69.2.

A cikin wata ukun da ya wuce Manchester United ta samu kudin da ita ma ba ta taba samu ba fam miliyan 581, yayin da ita ma Manchester City ta sanar da nata cinikin na fam miliyan 473.4, amma ita City na tsawon wata 13 ne.

Shugaban Chelsea Bruce Buck ya ji dadi ganin cewa kungiyar ta yi nasara a wasanninta kamar yadda ta yi a fannin kasuwanci a shekarar.

Chelsea ta ce tana sa ran kudin da take samu ya karu a kakar da ake ciki ta 2017/18 saboda sun dawo gasar cin kofin zakarun Turai, tare kuma da sake kulla yarjejeniya da kamfanin yin kayan wasa na Nike.