Real Madrid ta koma atisayen tunkarar 2018

Hakkin mallakar hoto Real Madrid
Image caption Real Madrid ta lashe kofi biyar a 2017

A ranar Asabar Real Madrid ta koma atisaye a filinta na Valdebebas domin shirin tunkarar kalubalen 2018.

Real mai rike da kofin La Liga da na Zakarun nahiyoyin duniya, ta buga wasan karshe a 2017 da Barcelona, inda Barca ta yi nasara da ci 3-0.

Magoya bayan kungiyar sama da 5,000 ne suka sayi tikiti domin ganin atisayen Madrid wadda ta shirya baje kolin kofi biyar da ta lashe a 2017.

Real Madrid ta ci kofin La Liga da na Zakarun Turai da Uefa Super Cup da Spanish Super Cup da na Zakarun nahiyoyin duniya.

Real Madrid wadda ke mataki na hudu a kan teburin La Liga tana da maki 31 da kwantan wasa daya.

Real za ta buga wasan farko da Numancia a gasar Copa del Rey ranar 4 ga watan Janairun 2018, sannan ta ziyarci Celta Vigo a gasar La Liga a ranar 7 ga watan Janairun.

Sai a ranar 13 ga watan Fabrairu ne Real Madrid za ta karbi bakuncin Paris St Germain a Santiago Bernabeu.

Labarai masu alaka