Salah ya ceci Liverpool a wajen Leicester

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salah ya ci kwallo 17 a gasar Premier ta shekarar nan

Liverpool ta yi nasarar doke Leicester City da ci 2-1 a wasan mako na 21 a gasar Premier da suka fafata a ranar Asabar a Anfield.

Tun farko Leicester City ce ta daga ragar Liverpool ta hannun Jamie Vardy, kuma haka aka je hutun rabin lokaci Leicester nada kwallo daya a raga.

Bayan da aka dawo ne Mohamed Salah ya farke ya kuma kara ta biyu a raga, kuma jumulla ya ci 17 a gasar ta Premier.

Wannan ne karon farko da Jurgen Klop ya yi nasarar doke Leicester City, bayan kashi da ya sha a wasa uku a baya.

Liverpool za ta jiyarci Burnley a wasan mako na 22 a gasar ta Premier, yayin da Leicester City za ta karbi bakuncin Huddersfield Town.