Nike ya yi tallar rigar Barca dauke da sunan Coutinho

Nike Hakkin mallakar hoto Nike Website
Image caption Liverpool ba ta sallama tayi biyu da Barcelona ta yi wa Coutinho a lokacin bazara ba

Kamfanin da yake yi wa Barcelona kayayyakin wasa, Nike ya yi tallar rigar kungiyar dauke da sunan dan kwallon Liverpool, Philippe Coutinho.

A jerin sunayen 'yan kwallon da Nike ya rubuta a jikin rigar wadda ya wallafa a shafinsa na Intanet ya ce ''Philippe Coutinho ya shirya bayyana a Camp Nou'', sai dai kuma ya goge rubutun daga baya.

Coutinho dan kwallon Brazil, mai shekara 25, yana saka kayan wasa na kamfanin Nike, wanda ke daukar nauyin dan kwallon.

Coutinho ya bukaci koma wa Barcelona a lokacin bazara, kuma ana rade-radin cewar zai koma Camp Nou a watan Janairu, idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallon ta Turai.

Liverpool taki sallama tayin da Barcelona ta yi wa dan kwallon kan fam miliyan 72 da fam miliyan 90 a lokacin bazarar.

BBC ta tuntubi kamfanin Nike da Barcelona don karin bayani.

Labarai masu alaka