Karim Benzema zai yi jinya

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Benzema bai yi atisayen da Real Madrid ta fara a ranar Asabar ba

Dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema zai yi jinya, sakamakon raunin da ya ji a wasan hamayya da Barcelona wanda ake yi wa lakabi da El Clasico.

Real ba ta bayyana ranar da Benzema zai dawo fagen tamaula ba, bisa raunin da ya yi a kafarsa ta hagu ba.

Sai dai kuma ana rade-radin cewar dan kwallon ba zai buga wasan Copa del Rey da Real za ta yi da Numancia gida da waje da karawa da Celta Vigo a gasar La Liga da watakila fafatawa da Villarreal da kuma Deportivo La Coruna ba.

Benzema bai halarci atisayen da Madrid ta fara a ranar Asabar ba, sai da likitocin kungiyar sun duba girman raunin da ya yi a ranar 23 ga watan Disamba.

Real Madrid wadda ta ci kofi biyar a 2017, tana ta hudu a kan teburin La Liga, za kuma ta buga wasan zagaye na biyu da Paris St Germain a gasar Zakarun Turai a watan Fabrairu.

Labarai masu alaka