Zan dauko fitattun 'yan kwallo — Wenger

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal tana mataki na biyar a kan teburin Premier, ita kuwa Chelsea tana matsayi na hudu

Kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce zai kawo kwararrun 'yan kwallon da za su maye gurbin Alexis Sanchez da Mesut Ozil da zarar sun bar kungiyar.

Wenger ya ce babu wata kungiya kawo yanzu da ta mika bukatar daukar 'yan wasan, amma ya ce Gunners ba za ta girgiza idan 'yan kwallon biyu suka bar ta ba.

A karshen kakar shekarar nan kwantiragin Sanchez da Ozil zai kare a Arsenal, kuma yanzu haka za su iya tattauna da kowacce kungiyar da ba ta buga gasar Premier a Janairun nan.

Arsenal na son yin zawarcin sabbin 'yan kwallo a watan Janairu, amma Wenger ya ce zai dan jira yaga makomar Sanchez da Ozil a kungiyar.

Haka kuma Wenger ya yi watsi da batun da ake yi cewar Arsenal za ta sayi David Luiz na Chelsea da dan kwallon Monaco, Thomas Lemar.

Arsenal za ta karbi bakuncin Chelsea a ranar Laraba a gasar Premier wasan mako na 22.

Labarai masu alaka