Salah da Mane za su halarci bikin CAF — Klopp

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool za ta fafata da Everton a gasar cin Kofin FA a ranar Alhamis

Kocin Liverpool, Jurgen Klop ya ce martabawa ce Mohamed Salah da Sadio Mane su halarci bikin gwarzon dan kwallon kafar Afirka da za a yi a Ghana.

Salah da Mane suna cikin 'yan wasa ukun da ke takarar kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2017 da hukumar kwallon kafar Afirka, CAF za ta karrama a ranar Alhamis.

'Yan wasan biyu za su halarci taron ne awa 24 kafin Liverpool ta fafata da Everton a gasar cin kofin FA.

Klopp ya ce ya san mahimmacin bikin da kyautar ga 'yan wasan, domin a lokacin da yake Borussia Dortmund bai hana Pierre-Emerick Aubameyang zuwa taron da aka yi a Nigeria ba.

Za a yi bikin zabar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na 2017 a Accra, Ghana, inda Sadio Mane da Mohamed Salah dukkan su daga Liverpool da Pierre-Emerick Aubameyang na Borussia Dortmund suke takara.

Labarai masu alaka