An tuhumi Wenger da kalamun batanci

Arsenal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ta tashi 1-1 da West Brom a wasan mako na 21 a gasar Premier a ranar Lahadi

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta tuhumi Arsene Wenger da kalamun batanci, bayan da Arsenal ta tashi wasa 1-1 da West Brom a gasar Premier a ranar Lahadi.

Ran Wenger ya baci matuka a lokacin da alkalin wasan tamaula Mike Dean ya bai wa West Brom bugun fenariti daf da za a tashi wasa ta kuma farke kwallon da aka zura mata tun farko.

Hukumar ta FA ta ce Wenger mai shekara 68, ya kalubalanci alkalan wasan a dakinsu na canja kaya da rashin gaskiya da rashin iya gudanar da aikinsu.

Hukumar ta Ingila ta bai wa Arsenal Wenger zuwa yammacin Juma'a, domin ya kare kansa.

Arsenal wadda ke mataki na biyar a kan teburin Premier, za ta kara da Chelsea wadda ke matsayi na uku a kan teburi a ranar Laraba.

Labarai masu alaka