Perez ya bukaci Real ta ci gaba da samun nasarori

Real Madrid Hakkin mallakar hoto RealMadrid FC
Image caption Kofi biyar Real Madrid ta lashe a shekarar 2017

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez ya bukaci Real Madrid da ta ci gaba da samun nasarori kamar yadda ta yi a shekarar 2017.

Real ta lashe kofi biyar a shekarar da ta wuce da suka hada da Kofin Zakarun Turai da na La Liga da UEFA Super Cup da Spanish Super Cup da na Zakarun nahiyoyin duniya.

Perez ya ce shekarar 2017 mahimmiya ce ga 'yan wasa da jami'ai da magoya bayan Madrid kan rawar da ta taka, yana kuma fatan za ta dora a inda ta tsaya.

Real Madrid wacce ke mataki na hudu a gasar La Ligar Spaniya, mai kwantan wasa daya, za ta ziyarci Numanci a fafatawar farko a gasar Copa del Rey a ranar Alhamis.

Haka kuma a cikin watan Fabrairu ne Real Madrid za ta kece-raini da Paris St-Germain a wasan zagaye na biyu a gasar cin Kofin Zakarun Turai.

A kuma ranar 7 ga watan Janairun 2018 Real Madrid za ta ziyarci Celta Vigo a wasan La Liga.

Labarai masu alaka