CAF: Salah da Mane za su Ghana

Mohamed Salah da Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mohamed Salah da Sadio Mane

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce domin nuna karamci, zai bar Mohamed Salah da Sadio Mane su halarci bukin bayar da kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a kasar Ghana.

Za su halarci bukinne kwana guda kafin wasan Liverpool din da Everton a gasar cin kofin FA a ranar Juma'a.

Salah da Mane na daga cikin 'yan wasa uku da hukumar CAF ta kebe domin bai wa daya daga cikinsu kyautar gwarzon dan kwallon Afrika a bukin da za a yi a ranar Alhamis.

"Za mu kwana a otal, su kuma za su kwana a cikin jirgin sama. Bambamcin kenan," in ji Klopp.

Mutum na uku da aka kebe domin samun kyautar shi ne dan kwallon Borussia Dortmund da Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang.

Mohamed Salah ne gwarzon dan kwallon kafar BBC