Ousmane Dembele zai koma murza leda

Ousmane Dembele a lokacin da ya ji rauni Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ousmane Dembele a lokacin da ya ji rauni

Watakila dan kwallon da ya fi kowanne tsada a kungiyar Barcelona, Ousmane Dembele zai koma murza leda a wannan makon bayan ya shafe kusan watanni hudu yana jinya.

Dan kwallon mai shekaru 20, ya koma Barcelona ne a kan fan miliyan 97 a cikin watan Agusta, amma sai ya ji rauni bayan ya buga wasanni uku kacal.

An yi wa dan wasan na Faransa tiyata a Finland kuma watakila a ranar Alhamis ya buga wasansa na farko tsakanin Barca da Celta Vigo a gasar Copa del Rey.

Dembele wanda aka siyo daga Borussia Dortmund, shi ne dan kwallo na biyu mafi tsada a duniya.

Hakkin mallakar hoto LLUIS GENE Getty Images/AFP
Image caption Dembele tare da Pique a lokacin horo

Dan kwallon Paris St-Germain, Neymar shi ne mafi tsada a duniya inda aka siyo shi daga Barcelona a kan fan miliyan 200.