CHAN 2018: Super Eagles ta fitar da 'yan wasa 23

Super Eagles Hakkin mallakar hoto The NFF
Image caption Nigeria ta yi ta uku a gasar kofin Afirka da aka yi a 2014

Kocin tawagar kwallon kafa ta Nigeria, Salisu Yusuf ya bayyana 'yan wasa 23 da za su buga wa kasar gasar cin Kofin nahiyar Afirka ta 'yan kwallon da ke wasa a gida.

Nan da 'yan kwanaki ne tawagar ta Nigeria za ta isa Morocco domin ci gaba da shirye-shiryen tunkarar kalubalen da ke gabanta.

Super Eagles za ta buga wasan farko da Rwanda a ranar 16 ga watan Janairu, sannan ta fafata da Libya a ranar 19 ga watan, sai kuma ta kece raini da Equatorial Guinea a ranar 23 ga watan Janairun 2018.

Ga jerin 'yan wasa 23 da za su buga wa Nigeria wasa:

Masu tsaron raga: Ikechukwu Ezenwa (Enyimba FC); Oladele Ajiboye (Plateau United); Theophilus Afelokhai (Enyimba FC)

Masu tsaron baya: Osas Okoro (Rangers International); Daniel James Itodo (Plateau United); Kalu Orji Okogbue (Rangers International); Ikouwem Utin (Enyimba FC); Abdullahi Musa (Wikki Tourists); Timothy Danladi (Katsina United); Ifeanyi Nweke (Kano Pillars); Stephen Eze (Kano Pillars)

Masu wasan tsakiyas: Ifeanyi Ifeanyi (Akwa United); Rabiu Ali (Kano Pillars); Augustine Oladapo (Enyimba FC); Ekundayo Ojo (Sunshine Stars)

Masu cin kwallo: Emeka Atuloma (Rivers United); Anthony Okpotu (Lobi Stars); Eneji Moses (Plateau United); Ibrahim Mustapha (Enyimba FC); Emeka Ogbuh (Rivers United); Sunday Faleye (Akwa United); Nura Muhammed (El-Kanemi Warriors); Okechukwu Gabriel (Akwa United)