''Bai kamata Liverpool ta sayar da Coutinho ba''

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sau uku Liverpool ba ta sallama tayin da Barcelona ta yi wa Coutinho ba

Tsohon dan wasan Liverpool, Jamie Carragher ya ja kunnen Liverpool da kar ta kuskura ta sayar wa da Barcelona Philippe Coutinho a watan Janairun nan.

Carragher tsohon mai tsaron bayan Liverpool ya ce bai kamata dan kwallon ya bar Anfield a yanzu ba, amma zai iya barin kungiyar a karshen kakar nan.

Wasu rahotanni na cewa Coutinho yana fatan ya koma Barcelona da murza-leda a watan nan, inda har wasu ke cewa ya buga wa Liverpool wasan karshe.

Rahotanni daga Spaniya na cewa Barcelona za ta sake taya dan kwallon na Brazil a watan Janairu, sai dai Liverpool ta ce har yanzu babu wata kungiya da ta mika mata bukatar hakan.

Barcelona ta taya Coutinho har karo uku a lokacin bazara, inda Liverpool ta ki sallama tayin da ta yi.

Labarai masu alaka