Arsenal da Chelsea sun raba maki bayan sun tashi 2-2

Jack Wilshere yana murnar bal din da ya ci Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jack Wilshere ya ci bal dinsa ta farko a gasar Premier tun watan Mayu na 2015

Hector Bellerin ya farke wa Arsenal bal din da ta ba ta damar raba daidai a maki da Chelsea ana dab da tashi a daya daga wasannin da suka fi kayatarwa a Premier a bana, inda suka tashi 2-2.

Kungiyoyin biyu sun yi ta kai wa juna hari kusan sau 30 a tsakaninsu, inda maso tsaron ragarsu Petr Cech na Arsenal da kuma Thibaut Courtois na Chelsea suka yi ta kokarin hana ci, in banda hudu da aka yi nasarar daga ragar da su.

Courtois ya yi kokari sosai wajen hana Alexis Sanchez da Alexandre Lacazette daga ragarsa, kafin dai daga karshe Jack Wilshere ya yi nasarar jefa masa kwallon a minti na 63.

Nasarar ba ta yi karko ba domin minti hudu tsakani ne sai Eden Hazard ya rama wa Chelsea da bugun fanareti, bayan da alkalin wasa ya hura cewa Hector Bellerin ya doke shi da kafa.

Chelsea ta yi tsammanin ta yi galaba ke nan a wasan lokacin da Marcos Alonso ya ci musu ta biyu a minti na 84.

Amma sai murna ta koma ciki lokacin da ana dab da tashi a cikin karin lokacin da aka bata, sai kawai Bellerin ya sheko wata bal, wadda ba ta zame ko ina ba sai cikin ragar Chelsea, aka tashi 2-2.

'Yan dakikoki kadan a kammala wasan Chelsea ta ga samu kuma ta ga rashi lokacin da Zappacosta ya sheka wa golan Arsenal bal ta doki karfen saman raga.

Yanzu Chelsea tana matsayi na uku da maki 46 a teburin na Premier, yayin da Arsenal ke matsayi na shida da maki 39.