Ashley Cole ya tsawaita kwantaraginsa a LA Galaxy

Cole has made 55 appearances for Los Angeles Galaxy Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Cole ya buga wa Los Angeles Galaxy wasa 55

Tsohon mai tsaron gidan Ingila Ashley Cole ya sanya hannun kan kwantaragin karin shekara daya a kungiyar kwallon kafa ta Los Angeles Galaxy.

Cole, mai shekara 37, ya koma Galaxy ne a watan Janairun 2016 kuma ya buga wasa 55 a kakar wasa biyu.

Tsohon dan wasa na Arsenal da Chelsea ya buga wa Ingila wasa 107 sai dai ya daina yin tamaular duniya bayan an ki sanya shi cikin tawagar da ta buga gasar cin Kofin Duniya ta 2014.

Kocin kulob din Sigi Schmid ya ce Cole "ya jajirce wajen shugabancin 'yan wasanmu. Ya nuna cewa zai iya yin nasara a wasan lig kuma muna fatan zai ci gaba da fafatawa mai kyau a kakar wasannin da ke tafe".

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba