Zidane ya cika shekara biyu a Real Madrid

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zidane ya ci kofi takwas a shekara biyu da ya yi yana jan ragamar Real Madrid

Mai horar da Real Madrid, Zinadine Zidane ya cika shekara biyu yana jan ragamar kungiyar.

Zidane ya karbi aikin kocin Real Madrid a ranar 4 ga watan Janairun 2016, bayan da kungiyar ta sanar da korar Rafa Benitez.

Tun kafin Zidane ya horar da Real Madrid sai da ya fara jan ragamar karamar kungiyar wadda ya fara aiki da ita a watan Yunin 2014.

Kwana biyar da Zidane ya karbi aikin kocin Real Madrid ya ja kungiyar wasansa na farko a La Liga inda Real ta ci Deportivo La Coruna 5-0.

Haka kuma a ranar 28 ga watan Mayu Real ta dauki kofin Zakarun Turai na 11, bayan da ta ci Atletico Madrid a bugun fenariti.

A ranar 18 ga watan Satumbar 2016, Real Madrid ta ci Espanyol 2-0 a La Liga, inda ta yi wasa 16 a gasar ba tare da an doke ta ba.

Haka kuma a ranar 18 ga watan Disamba 2016, Real Madrid ta doke Kashima Antlers 4-2 ta kuma lashe kofin zakarun nahiyoyin duniya.

Zidane ya kafa tarihin lashe wasa 40 ba tare da an doke Real ba a ranar 12 ga watan Janairun 2017, bayan da ta yi canjaras da Sevilla a wasa na biyu a gasar Copa del Rey.

A ranar 3 ga watan Yunin 2017, Zidane ya ja ragamar Real Madrid ta doke Juventus 4-1 ta kuma ci Kofin Zakarun Turai na 12 a tarihi sannan ta lashe La Liga a kakar shekarar.

A dai cikin shekarar 2017 kocin ya lashe Uefa Super Cup da Spanish Super Cup da kofin Zakarun nahiyoyi, sannan aka zabe shi kocin da babu kamarsa a 2017.

Labarai masu alaka