Coutinho ba zai buga karawa da Everton ba

Liverpool Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool ce ta sanar da cewar Coutinho yana jinyar rauni

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce Philippe Coutinho ba zai buga wasan kalubale da kungiyar za ta kara da Everton a ranar Juma'a ba, sakamakon raunin da yake jinya.

BBC ta fahimci cewar a kowanne lokaci Barcelona za ta taya dan kwallon tawagar Brazil mai shekara 25.

Coutinho bai buga wasan da Liverpool ta doke Burnley ba, kuma Klopp ya ce babu abinda zai ce domin sai ya zama babban labari.

Sau uku Liverpool ba ta sallama tayin da Barcelona ta yi wa Coutinho tun kafin a fara kakar kwallon kafa ta bana.

Mohamed Salah da Sadio Mane ba za su buga karawar ba, sakamakon bikin gwarzon dan kwallon Afirka da suke takara da za a karrama a Acca, Ghana a ranar Alhamis.

Labarai masu alaka