Everton ta dauki Tosun daga Besiktas

Everton Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Everton za ta kara da Liverpool a wasan hamayya a gasar kalubale a ranar Juma'a

Everton da Besiktas sun kammala yarjejeniyar cinikin Cenk Tosun, har ma an shiga tattaunawa da dan kwallon kan kunshin kwantiragi in ji Sam Allardyce.

A ranar Laraba Everton ta fara tuntubar shugaban Besiktas, Fikret Orman kan cinikin dan wasan mai cin kwallo da ake cewar ya kai fan miliyan 27.

Tosun mai shekara 26, yana Landan domin saka hannu a kunshin yarjejeniyar da Everton za ta gabatar masa idan ya amince.

Allardyce ya ce yana fatan za su kammala daukar dan wasan a kan lokaci domin ya buga musu karawar da za su yi da Liverpool a gasar kofin FA a ranar Juma'a

Labarai masu alaka