Premier: Tottenham da West Ham sun yi 1-1

Son Heung-min alokacin da ya farke wa Tottemham Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Saura minti shida lokaci ya cika Son Heung-min ya ceci Tottenham

Tottenham da West Ham United sun yi kunnen doki 1-1 a wasansu na Premier na mako na 22, inda Pedro Obiang da Son Heung-min ko wanne ya ci wa kungiyarsa.

Pedro Obiang ya fara ci wa West Ham wadda ta kai bakunci a minti na 70 bayan da ya sheko bal din tun daga tazarar yadi 35, ba ta tsaya a ko ina ba sai a cikin ragar Tottenham.

Haka ana ci gaba da wasa har zuwa minti 14 inda daga nan ne kuma shi ma Son Heung-min ya kwatanta irin yadda aka ci su, ya kwararo kwallon daga nisan yadi 30 shi kuma, ta kwana a ragar West Ham.

Tottenham ta ci gaba da zama a teburin na Premier a matsayin ta biyar da maki 41, yayin da West Ham ta daga zuwa mataki na 15 da maki 22.

A ranar Lahadi Tottenham za ta karbi bakuncin AFC Wimbledon (15:00 GMT) a wasan cin kofin FA, zagaye na uku, yayin da West Ham a ranar za ta je irin wasan a Shrewsbury sa'a daya kafin na Tottenham.