Copa del Rey: Barcelona ta yi 1-1 da Celta Vigo

Ousmane Dembele na Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wannan shi ne wasa na hudu da Ousmane Dembele ya yi wa Barcelona

Ousmane Dembele ya dawo wasa bayan jinyar da ya yi, inda Barcelona ta yi kunnen doki 1-1 da Celta Vigo a wasan farko na cin kofin Copa del Rey matakin kungiyoyi 16.

Matashin dan wasan mai shekara 20 wanda ta sayo a kan fam miliyan 96 da dubu 800 a farkon kakar nan ya shigo wasan ne a cikin minti 20 na karshe.

Wannan shi ne wasansa na farko tun lokacin da ya tafi jinyar raunin da ya ji a cinya a ranar 16 ga watan Satumba.

Barca ce ta fara daga raga a wasan ta hannun dan wasanta na gaba na karamar tawagarta Jose Arnaiz, a minti na 15.

Sai dai kuma Pione Sisto ya farke wa masu masaukin, Celta Vigo a minti na 31, kuma Iago Aspas ya kai harin da bal din ta doki tirken ragar Barcelona.

'Yan Barcelona Sergio Busquets da Sergi Roberto kowannensu ya kai mugun harin da bal din ta doki tirken raga amma ba ta ci ba.

A ranar Alhamis 11 ga watan nan na Janairu ne za a yi karo na biyu na wasan a gidan Barcelona, Nou Camp.