Copa del Rey: Real Madrid ta ci Numancia 3-0

Gareth Bale na buga fanareti Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gareth Bale na wasansa na farko ke nan a cikin wata uku

Gareth Bale ya dawo wasa da sa'a bayan raunin da ya yi jinya, inda ya fara ci wa Real Madrid bal a wasansu na karon farko da Numancia na cin kofin Copa del Rey matakin kungiyoyi 16, inda suka yi galaba da ci 3-0.

Rabon Bale da cin bal a Spaniya tun watan Satumba, sai wannan wasan da ya ci bugun fanareti da ta zama bal ta biyar da ya ci a bana.

Ana daidai sa'a daya da wasan alkalin wasa ya kori dan wasan Numancia, wadda ke matsayi na biyar a gasar Spaniya ta biyu, Pape Maly Diamanka.

Daga nan ne kuma Isco ya kara cin wani bugun fanaretin, sannan Borja Mayoral ya ci bal ta uku da ka.

A La Liga wasa shida kawai Bale ya yi a kakar bana saboda rauni da yake ji.

Real a gidanta za ta nemi samun gurbin wasan dab da na kusa da karshe a gasar ta Copa del Rey, a wasan da za su sake yi na biyu da Numancia a ranar Laraba mai zuwa.