George Weah ya gayyaci Arsene Wenger bikin rantsar da shi

George Weah, file photo taken on April 28, 2016 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption George Weah ya taka leda a Monaco lokacin da Arsene Wenger ke kocin kungiyar

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya shaida wa BBC cewa zababben shugaban kasar Liberia George Weah ya gayyace shi bikin rantsar da shi wanda za a yi nan gaba a wannan watan.

Wenger ne kocin Monaco tsakanin 1988 zuwa 1992 loacin da Weah ke murza leda a kungiyar.

Kocin ya ce ba shi da tabbacin halartar bikin.

"George ya gayyace ni zuwa bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa. Sai dai na yi amannar cewa al'amura za su sha gabana a lokacin amma idan aka dakatar da ni daga aiki (saboda sukar da ya yi wa alkalan wasa) zan samu lokacin zuwa bikin."

Wenger na fuskantar horo daga hukumar kula da kwallon kafar Ingila saboda sukar da ya rika yi wa alkalan wasa a makonnin baya bayan nan.

Kocinna Arsenal ya ce har yanzu yana mamakin irin nasarorin da Weah ya samu a rayuwarsa.

"Rayuwar [Weah] tamkar wasan kwaikwayo ce. Wani lokacin sai na ji kamar ba gaske ba. Zan iya tsaya fim a kan rayuwarsa," in ji Wenger wanda ke cike da murna.

"Zan iya tuna karon farko da na gan shi a Monaco, ya zo ba tare da sanin kowa ba, kuma babu wata kungiyar da ta jinjina masa amma a haka ya zama gwarzon dan kwallon duniya na shekarar 1995 yanzu kuma ya zama shugaban kasa".

Wenger also recalled the passion and love Weah had for Liberia.

Weah ya lashe zaben shugaban kasar Liberia a zagaye na biyu a watan jiya, bayan ya kayar da abokin hamayyarsa Joseph Boakai inda ya samu kashi 60 cikin 100 na kuri'ar da aka kada.

Zai maye gurbin Ellen Johnson Sirleaf, macen farko da ta zaman shugabar kasa a Africa.

Labarai masu alaka

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba