Man United ta kai mataki na gaba a kofin FA bayan doke Derby 2-0

Jesse Lingard Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Bal din da Jesse Lingard ya ci a kusan karshen lokaci, ita ce ta karya lagon 'yan wasan Derby

Manchester United ta yi jinkiri wajen doke Derby County a wasan da ya kayatar na cin kofin FA, na zagaye na uku a Old Trafford, da ci 2-0.

Da farko dai wasan ya nuna cewa kusan sai kungiyoyin sun yi karo na biyu kafin a samu gwani, kafin Romelu Lukaku ya ajiye wa Jesse Lingard, wata bal a daidai, wadda bai yi wata-wata ba ya sheka ta a raga a minti na 84 daga tazarar yadi 20.

Haka kuma a daidai minti 90 na wasan ne shi ma Lukakun wanda aka sako shi bayan hutun rabin lokaci, ya canji Mkhitaryan, ya daga raga, da bal ta biyu, bayan wani ba-ni-in-ba-ka da ya yi da Anthony Martial.

Dan wasan gaba na United din Marcus Rashford ya kuskure ci a kashin farko na wasan da kuma na biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, inda bal din ke dukan tirken raga.

Mai tsaron ragar bakin Scott Carson ya yi kokari sosai, inda sau takwas yana kade hare-haren da kusan ba makawa da United ta ci.

Kungiyar ta Derby, wadda ke matsayi na biyu a teburin gasar Championship, ta kasa da Premier, ta yi wasa da kyau, inda dan wasanta Tom Lawrence ya kai wa United wani kyakkyawan hari wanda mai tsaron ragar kungiyar ta Mourinho, Sergio Romero ya yi kwance-kwance ya kare.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jose Mourinho yana da sama da mako daya ya shirya wa wasansa na gaba na Premier

Bayan da United ta sha kashi a wurin abokan hamayyar Derby din na neman tsallakawa zuwa gasar Premier, Bristol City a kofin lig na Carabao, Jose Mourinho ya yi sauyi domin ganin ba a sake fitar da su ba a wannan gasar ma, inda ya zuba 'yan wasa manya, duk da cewa ya yi canji biyar.

Kasancewar maki 15 ne tsakanin United da Manchester City ta daya a Premier kuma United din ba ta cikin wadanda ake ganin za su iya samun gurbin gasar zakarun Turai, kofin FA din shi ne ake ganin za ta iya dauka a kakar nan.

Manchester United tana da kwana goma a yanzu kafin ta yi wasanta na gaba a gida, a gasar Premier da Stoke City ranar Litinin, 15 ga watan Janairu da karfe 9:00 na dare agogon Najeriya.

Ita kuwa kungiyar Derby za ta je gidan Birmingham a gasarsu ta Championship ranar Asabar mai zuwa. Inda za su fafata da karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.