Kofin FA: Van Dijk ya fara da sa'a a Liverpool da ta doke Everton 2-1

Jurgen Klopp da Virgil van Dijk Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Van Dijk wanda ya kafa tarihin zama dan wasan baya da aka saya da kudi mafi yawa a duniya, ya fara da kai Liverpool zagaye na gaba a gasar kofin FA

Virgil van Dijk ya fara wasansa a Liverpool da sa'a bayan da ta sayo shi a kan fam miliyan 75 daga Southampton, inda a kusan lokacin tashi ya taimaki sabuwar kungiyar tasa da cin da ta doke Everton 2-1 a wasan hamayya na zagaye na uku na kofin FA.

A fafatawar da aka yi a gidan Liverpool Anfield, kusan Everton na kan hanyar kai wasan karo na gaba a gidanta Goodison Park, kafin mai tsaron ragar bakin Jordan Pickford ya yi kuskuren fahimtar kwanar da aka dauko ya bari Van Dijk, ya ci shi da ka saura minti shida lokaci ya cika.

Bal din ta biyu wadda dan bayan mafi tsada, wanda ba a taba kashe kudi mai yawa aka sayo wani dan baya ba a duniya, ya ci ita ba wa Liverpool kaiwa zagaye na hudu na gasar ta cin kofin FA.

Gylfi Sigurdsson ne ya farke wa Everton a minti na 67, bayan da tun da farko James Milner ya ci wa Liverpool da fanareti, minti 10 kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Alkalin wasa Bobby Madley wanda ya yi faman gaske a alkalancin wasan na hamayya kamar yadda daman aka saba yi a karawar, ya ba wa Liverpool fanareti ne sakamakon ketar da Mason Holgate ya yi wa Adam Lallana.

Liverpool ta yi wasan ne ba tare da dan gabanta ba, gwarzon dan kwallon kafar Afirka na Caf na 2017, Mohamed Salah, wanda yake jinya, da kuma gwanin dan wasanta na tsakiya Philippe Coutinho, wanda ake cewa zai koma Barcelona a kan fam miliyan 140.

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp bai bata lokaci ba wajen fara amfani da sabon dan wasansa na baya Van Dijk, bayan da suka siyo shi daga Southampton - sai dai dan wasan na Holland mai shekara 26 a gaba a fara aikinsa, da cin bal din ta biyu, wadda ta kai su zuwa mataki na gaba a gasar ta kofin FA.

A wasanni na gaba dukkanin kungiyoyin biyu za su fafata ne a gasar Premier, inda Everton za ta je gidan Tottenham ranar Asabar, 13 ga watan Janairu da karfe 6:30 na yamma agogon Najeriya.

Ita kuwa Liverpool sai washe-gari ne (Lahadi) za ta karbi bakuncin jagora a gasar ta Premier Manchester City da karfe 5:00 na yamma agogon Najeriya.