Mourinho ya bai wa Mkhtaryan hakuri

Manchester United Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manchester United tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Jose Mourinho ya ce ya bai wa Henrikh Mkhitaryan hakuri bayan da ya sauya shi a karawar da Manchester United ta doke Derby da ci 2-0 a ranar Juma'a.

Mourinho ya canja Mkhitaryan, dan kwallon Armenia da Romelu Lukaku bayan minti 45 din farko a wasan babu ci a gasar kofin FA fafatawar zagaye na uku.

Rabon da Mkhitaryan ya ci wa United kwallo tun a watan Satumba, kuma sau biyu ne aka fara wasa da dan kwallon aka kuma kammala da shi.

Mourinho ya ce bai ji dadin abin da ya yi ba, bai kamata ya sauya dan wasan ba, domin yana kokari yana kuma taka rawar gani matuka.

Kocin ya kara da cewar a zuciyarsa ce ta ayyana cewar Rashford ba zai ci kwallo ba a karawar, saboda haka ya yanke shawara sa Lukaku ya maye gurbin Micki.

Mourinho ya ce baya irin wannan sauyin a hutun rabin lokaci, ya kuma nemi afuwar Mkhitaryan a gaba mutane.

Labarai masu alaka