Coutinho bai bi Liverpool atisaye a Dubai ba

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool ta doke Everton a gasar cin kofin FA da suka kara a ranar Juma'a a Anfield

Dan kwallon Brazil, Philippe Coutinho bai bi Liverpool atisayen da taje yi a Dubai na dan karamin lokaci ba.

Kamfanin dillacin labarai na PA ya ce ya fahimci cewar Coutinho yana jinyar rauni kuma yana daga cikin manyan 'yan wasan da kungiyar ta amince suyi zamansu a Merseyside.

Rahotanni na cewar Barcelona na daf da sake taya dan kwallon a cikin watan Janairu kan fam miliyan 140 domin ya koma Spaniya da murza-leda.

Sau uku Liverpool ba ta sallama tayin da Barca ta yi wa Coutinho ba, tun kafin a fara kakar kwallon kafa ta shekarar nan.

Har yanzu Coutinho bai buga wa Liverpool tamaula ba tun lokacin da aka bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo ta Turai da ta fara ci a farkon watan Janairu.

Labarai masu alaka