'Yan Barcelona da za su fafata da Levante

Barcelona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Barcelona tana matsayi na daya a kan teburin La Liga da maki 45

Ernesto Valverde ya bayyana 'yan wasan Barcelona da za su kara da Levante a gasar cin kofin La Liga wasan mako na 18 a ranar Lahadi a Camp Nou.

Cikin 'yan wasan da ba za su buga wa Barca karawar ba sun hada da Paco Alcacer da Umtiti da kuma Arda Turan.

Haka kuma 'yan wasa kamar su Rafinha da Deulofeu da kuma Aleix Vidal na yin jinya, yayin da Busquets ke yin hutun hukuncin dakatar wa.

Bacerlona tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 45, ta kuma bai wa Atletico Madrid wadda ke matsayi na biyu tazarar maki shida.

Ga 'yan wasan da Barca ta bayyana:

Ter Stegen da Semedo da Pique da Rakitic da Denis Suarez da Iniesta da Suarez da Messi da Dembele da kuma Mascherano.

Sauran 'yan kwallon sun hada da Cillessen Paulinho da Jordi Alba da Digne da Roberto da André Gomes da Vermaelen da kuma Jose Arnaiz.