Carlos Tevez ya koma Boca Junior

Carlo Tevez Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tevez tsohon dan kwallon Manchester United da Manchester City ne

Dan wasan Argentina, Carlos Tevez ya koma Boca Junior, bayan da ya kasa taka rawar gani a Shanghai Shenhua.

Tevez tsohon dan wasan Manchester United da Manchester City, ya koma Shanghai a Disambar 2016 kan kudi fam miliyan 40.

Wannan ne karo na uku da Tevez zai buga wa Boca Junior tamaula, kungiyar da ya fara yi wa wasa tun yana matashin dan kwallo a shekarar 2001 zuwa 2004 da kuma tsakanin 2005 zuwa 2006.

Dan wasan ya ci kofin gasa takwas a kasashe hudu da ya murza-leda.

Labarai masu alaka