Coutinho ya koma Barca kan fam miliyan 142

Liverpool Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Liverpool ta doke Everton a gasar cin kofin FA a ranar Juma'a a Anfield

Philippe Coutinho ya koma Barcelona kan kudi fam miliyan 142, bayan da dan kwallon bai bi Liverpool wasan atisaye da ta je yi a Dubai ba.

Coutinho ya zama dan kwallo na biyu da aka saya mafi tsada a duniya, bayan Neymar da ya koma Paris St Germain daga Barcelona kan kudi fam miliyan 200 a bana.

Liverpool ba ta sallama tayi uku da Barcelona ta yi wa Coutinho ba, sannan ba ta bai wa dan kwallon izinin barin Anfield ba kamar yadda ya bukata kafin a fara kakar shekarar nan.

Tayi na karshe da Barcelona ta yi wa Coutinho shi ne fam miliyan 118 tun kafin a fara kakar tamaula ta bana.

Coutinho bai bi Liverpool atisayen da ta je Dubai ba, sakamakon jinyar raunin da yake yi, kuma bai buga wa kungiyar wasa biyu da ta buga ba.

Labarai masu alaka