Jose Mourinho karamin mutum ne - Antonio Conte

Antonio Conte Hakkin mallakar hoto Others
Image caption Antonio Conte ya ce maganar Mourinho a kansa ta nuna kociyan na United karamin mutum ne

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya kira takwaransa na Manchester United Jose Mourinho da cewa karamin mutum ne, a ci gaba da sukar juna da suke yi.

A ranar Juma'a, Mourinho ya yi wata magana da ake ganin da Conte yake, inda ya ce, shi ba za a taba dakatar da shi ba saboda laifin coge a wasa.

Shi dai Conte, an taba dakatar da shi wata hudu a lokacin da yake kociyan Juventus a kakar 2012-13 saboda kin bayar da rahoton yin cogen wasa a tsohuwar kungiyarsa Siena.

Amma kuma a shekara ta 2016, wata kotu ta wanke kociyan dan Italiya da cewa ba shi da wani laifi a kan batun.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jose Mourinho yana fushi da Antonio Conte tun lokacin da Chelsea ta doke United 4-0 a watan Oktoba na 2016

An ruwaito Conte yana cewa :"Ina jin idan kana irin wadannan kalamai, kalaman da za ka yi domin ka ci mutuncin wani, kuma ba ka san gaskiyar yadda maganar take ba, to sai in ce kai karamin mutum ne.''

Conte ya furta wannan kalami ne a lokacin da yake magana da BBC bayan wasan da kungiyarsa ta Chelsea ta tashi canjaras ba ci 0-0 a gidan Norwich a wasan kofin Fana zagaye na uku.

Conte ya sheda wa BBC cewa a lokacin da za su yi wasa da United zai yi kokarin yadda za su gana da Mourinho a daki, shi da shi kawai, domin bayani a kan wadannan kalamai, amma ya ce bai sani ba ko Mourinho din zai yadda su gana su kadai.