'Yan wasan Real 18 da za su fafata da Celta

La Liga Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Real Madrid tana matsayi na hudu a kan teburin La Liga da maki 31

Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa Real Madrid 18 da za su fuskanci Celta Vigo a gasar La Liga da za su kara a wasan mako na 18 a ranar Lahadi.

Real Madrid da Celta sun fafata sau hudu a kakar 2016/17, inda Madrid ta ci Celta 2-1 a gasar La Liga a ranar 27 ga watan Agustan 2016.

A gasar Copa del Rey da kungiyoyin suka fafata a ranar 18 ga watan Janairun 2017, Celta ce da doke Real da ci 2-1 a wasan farko, inda suka tashi 2-2 a gidan Celta a karawa ta biyu a ranar 25 ga watan Janairun 2017.

A wasa na biyu na cin kofin La Ligar shekarar kuwa, Real ce ta doke Celta da ci 4-1 a ranar 17 ga watan Mayun 2017.

Real Madrid mai kwantan wasa daya tana mataki na hudu a kan teburin La Liga da maki 31.

Ga 'yan wasan Madrid da suka ziyarci Celta:

Masu tsaron raga: Keylor Navas da Casilla da kuma Moha.

Masu tsaron baya: Vallejo da Varane da Nacho da Marcelo da Theo da kuma Achraf.

Masu wasan tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Asensio da Isco da kuma Kovacic.

Masu cin kwallo: Cristiano Ronaldo da Bale da Lucas Vazquez da kuma Borja Mayoral.

Labarai masu alaka