PSG na tuhumar Pastore da kuma Cavani

PSG Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Paris St-Germain tana ta daya a kan teburin Faransa da maki 50

Paris St-Germain na tuhumar Edison Cavani da Javier Pastore da yin lattin koma wa Faransa daga hutun da suka je yankin Latin Amurka.

Hakan ne ya sa 'yan wasan biyu ba za su buga wa kungiyar wasan cin kofin kalubalen kasar da za ta fafata da Rennes a ranar Lahadi ba.

Wata majiya ta kusa da kungiyar ta ce 'yan wasan biyu za su fuskanci hukunci mai tsauri ciki har da tara.

Cavani ya koma Faransa ranar Juma'a kwana biyu kungiyar ta fuskanci Rennes, yayin da Pastore har yanzu bai koma PSG ba.

Cavani ya ce ya so ya yi hutun sabuwar shekara tare da iyalansa, kuma ya samu matsala wajen samun jirgin da zai mayar da shi Faransa.

Shi kuwa Pastore ya shaida wa sashen wasanni na Yahoo cewa yana da matsalar da ta shafi iyali, ya kuma musanta cewa yana shirin barin kungiyar ne.

PSG tana mataki na daya a kan teburin gasar cin kofin Faransa da maki 50, bayan da ta buga wasa 19.

Labarai masu alaka