Forest ta fitar da Arsenal a FA Cup

FA Cup Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Arsenal ce mai rike da kofin FA da aka fitar da ita a wasan zagaye na uku

Kungiyar Nottingham Forest mai buga gasar Championship ta fitar da Arsenal a gasar cin kofin kalubalen Ingila, bayan da ta doke ta 4-2 a karawar da suka yi a ranar Lahadi.

Forest wadda ba ta da koci ce ta fara cin kwallo ta hannun Eric Lichaj, sai dai minti uku tsakani Arsenal ta farke ta hannun Per Mertesacker.

Forest wadda Gary Brazail ke jan ragamar kungiyar a matsayin rikon kwarya ta kara kwallo na biyu ta hannun Lichaj kafin aje hutun rabin lokaci.

Haka kuma an zura wa Arsenal kwallo na uku ta hannun Ben Brereton a bugun fenariti, bayan nan ne Danny Welbeck ya ci wa Gunners kwallo na biyu a wasan.

Forest ta ci kwallo na hudu ta hannun Kieran Dowell saura minti biyar a tashi daga fafatawar, bayan nan aka korar mata dan wasa Joe Worrall sakamakon keta da ya yi.

Rabonda a fitar da Arsenal a gasar FA a wasan zagaye na uku tun a watan Janairun 1996, bayan da Sheffield United ta yi nasara a kanta.

Labarai masu alaka